1 Maris 2017 - 12:23
Kasar Yamen Tana Fuskantar Matsalar Fari

Kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta sanar da cewa: Baya ga hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin masarautar Saudiyya ke ci gaba da kai wa kan Yamen, kasar kuma tana fuskantar matsalar fari.

A karshen ziyarar aikin da ya kai kasar Yamen a jiya Talata: Babban daraktan kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa Red Cross a yankin gabas ta tsakiya Robert Mardini ya bayyana cewa: A daidai lokacin da rumbun tsimin abincin kasar Yamen ke daf da karewa nan da watanni biyu zuwa hudu, a gefe guda kuma matsalar fari tana ci gaba da kunno kai a kasar lamarin da zai wurga rayuwar al'umma cikin mawuyancin hali a kasar.

Robert Mardini ya kara jaddada damuwarsa kan yadda kasar Saudiyya da kawayenta suka yi kawanya wa kasar Yamen tare da hana shigar da kayayyakin abinci da na bukatu ga al'umma da suke cikin halin kaka-ni ka yi musamman al'ummar garin Bandar-Jadid da ke yammacin kasar. 288